ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, a yayin da tattaunawar da shugaban Iran Ibrahim Ra’isi da kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron suka gudanar a yau ta wayar tarho har tsawon sa’a guda, sun tabo batutuwa da dama da suke da alaka huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa.
Ibrahim Ra’isi ya sheda wa Macron cewa, akwai abubuwa da dama da suka hada Faransa da Iran a bangarori daban-daban, wanda yin aiki tsakanin kasashen biyu zai sanya al’ummomin kasashen biyu su ci moriyar juna.
Haka nan kuma Ra’isi ya jaddada cewa, duk wata alaka tsakanin Iran da Faransa, dole ne ta ginu a kan girmama juna, da kuma kare maslahar juna.
Dangane da batun tattaunawar da ake gudanarwa domin raya yarjejeniyar nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, Ra’isi ya bayyana cewa, Amurka da kasashen turai su ne ya kamata su dawo su yi aiki da yarjejeniyar nukiliya domin raya ta.
Haka nan kuma ya jaddada cewa, Iran ba za ta yi wasa wajen kare hakkokinta ba a wannan yarjejeniya, kamar yadda kuma ya sanya batun janye wa Iran takunkuman da Amurka ta kakaba mata a matsayin daya daga cikin sharudda na dawowar Iran domin yin aiki da dukkanin bangarorin yarjejeniyar..
342/